ABNA24 : Ministan Yada Labarai Lai Mohammed ne ya bayyana hakan a lokacin day a halarci tashar jirgin kasa ta Obafemi Awolowo da aka gina kan sabuwar hanyar jirgin kasa daga Lagos zuwa Ibadan.
Ministan yada labaran na Najeriya ya ce “Babu wata babbar hanyar da ya kamata mu nuna wa masu korafi kan ciwo bashin da muke yi, kamar mu nuna musu wannan titin jirgin, domin su ga abin da muke yi da wadannan kudade.
Wannan furuci na zuwa ne a daidai lokacin wasu daga cikin ‘yan kasar suke kokawa kan yadda gwamnati take ciwo bashi na biliyoyin daloli daga waje, ba tare da sun gani a kasa ba.
342/